Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 2

Ayyukan Manzanni 2:4-15

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Dukansu suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka fara magana da wadansu harsuna, yadda Ruhu ya ba su iko su yi magana.
5A lokacin akwai Yahudawa dake zaune a Urushalima, mutanen Allah, daga kowace kasa karkashin sama.
6Da suka ji wannan kara jama'a duk suka taru suka rude saboda kowannensu ya ji suna magana da harshensa.
7Suka yi mamaki matuka; suka ce, “Lallai, wadannan duka ba Galiliyawa ba ne?
8Yaya mu ke jinsu duka, kowannensu na magana a cikin harshen da aka haife mu?
9Fisiyawa da Mediyawa da Elimawa, da Yahudawa da Kafadokiya, cikin Fontus da Asiya,
10cikin Firgia da Bamfiliya, cikin Masar da yankunan Libiya ta wajen Sur, da baki daga Roma,
11Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah.”
12Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, “Menene ma'anar wannan?”
13Amma wasu suka yi ba'a suka ce, “Sun bugu ne da sabon ruwan inabi.”
14Amma Bitrus ya tashi tare da sha dayan, ya daga murya ya ce da su, “Mutanen Yahuda da dukanku dake zaune a Urushalima, bari ku san wannan; ku saurari maganata.
15Domin wadannan mutanen ba buguwa suka yi ba yadda kuke zato, domin yanzu karfe tara ne na safe kawai.

Read Ayyukan Manzanni 2Ayyukan Manzanni 2
Compare Ayyukan Manzanni 2:4-15Ayyukan Manzanni 2:4-15