Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 2

Ayyukan Manzanni 2:10-44

Help us?
Click on verse(s) to share them!
10cikin Firgia da Bamfiliya, cikin Masar da yankunan Libiya ta wajen Sur, da baki daga Roma,
11Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah.”
12Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, “Menene ma'anar wannan?”
13Amma wasu suka yi ba'a suka ce, “Sun bugu ne da sabon ruwan inabi.”
14Amma Bitrus ya tashi tare da sha dayan, ya daga murya ya ce da su, “Mutanen Yahuda da dukanku dake zaune a Urushalima, bari ku san wannan; ku saurari maganata.
15Domin wadannan mutanen ba buguwa suka yi ba yadda kuke zato, domin yanzu karfe tara ne na safe kawai.
16Amma wannan shine abinda aka fada ta wurin annabi Yowel.
17Allah ya ce, 'Haka zai kasance a kwanakin karshe, zan zubo Ruhuna a kan dukan mutane, 'ya'yanku maza da mata za su yi anabci, kuma samarinku za su ga wahayoyi, kuma tsofaffinku za su yi mafarkai.
18Haka kuma a bisa bayi na maza da mata, a kwanakin nan zan zubo da Ruhuna, kuma za su yi anabci.
19Zan nuna al'ajibai a sararin sama da kuma alamu a bisa duniya, jini da wuta, da girgije.
20Rana zata juya ta koma duhu kuma wata ya koma jini, kafin Babbar ranan nan ta Ubangiji ta zo.
21Zai kuma zama dukan wanda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto.
22Mutanen Isra'ila, ku saurari wadannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar da shi gareku ta wurin manyan ayyuka da ban mamaki da alamu da Allah ya yi ta wurinsa a tsakiyarku, kamar yadda ku da kanku kuka sani.
23Saboda tabbataccen shiri da riga sani na Allah, aka bayar dashi, ku kuma, ta hannun mutane 'yan tawaye, kuka gicciye shi kuma kuka kashe shi.
24Wanda Allah ya tayar, bayan ya cire zafin mutuwa daga gareshi, saboda ba zai yiwu ba ta rike shi.
25Gama, game da shi, 'Ina ganin Ubangiji a gabana ko yaushe, domin yana gefen hannun damana saboda kada in firgita.
26Saboda haka zuciyata na farin ciki harshena yana yin murna. Kuma, jikina zai zauna gabagadi.
27Gama ba za ka watsar da raina a lahira ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka ya ga ruba ba.
28Ka bayyana mani hanyar rai; da fuskarka zaka cika ni da farin ciki.
29'Yan'uwa, zan yi magana da ku gabagadi game da baba Dauda: ya mutu kuma aka bizne shi, kuma kabarinsa na nan tare da mu har yau.
30Domin haka, don shi annabi ne kuma ya san Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa daga cikin zuriyarsa zai sanya wani bisa kursiyinsa.
31Ya hango wannan al'amari kuma ya yi magana game da tashin Almasihu, 'Ba ayi watsi da shi ba a lahira, kuma jikinsa bai ga rubewa ba.'
32Wannan Yesun - Allah ya tashe shi, wanda dukanmu shaidu ne.
33Saboda haka yadda aka tashe shi zuwa hannun dama na Allah kuma ya karbi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, shine ya zubo mana wannan da kuke gani kuma kuke ji.
34Dauda bai hau zuwa sama ba, amma ya ce, “Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna hannun dama na,
35har sai na maida makiyanka abin takawar sawunka.”'
36Saboda haka, bari gidan Isra'ila su sani tabbas wannan Yesun wanda kuka gicciye, Allah ya maishe shi Ubangiji da kuma Almasihu.
37Da suka ji haka sai suka soku a zukatansu, suka cewa Bitrus da sauran manzanni, “'Yan'uwa me za mu yi?”
38Sai Bitrus ya ce masu, “Ku tuba ayi wa kowannenku baftisma, cikin sunan Yesu Almasihu domin gafarar zunubanku, kuma za ku karbi baiwar Ruhu Mai Tsarki.
39Domin alkawarin a gareku ne da 'ya'yanku da duk wadanda ke nesa, dukan iyakar mutanen da Ubangiji Allahnmu zai kira.”
40Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, “Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara.”
41Sai suka karbi maganar sa kuma aka yi ma su baftisma, a wannan rana kuma aka sami karin rayuka wajen dubu uku.
42Su ka cigaba cikin koyarwar manzanni da zumunta, cikin kakkaryawar gurasa da kuma cikin addu'o'i.
43Tsoro ya sauko bisa kowane rai, kuma aka yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin.
44Duka wadanda suka ba da gaskiya suna tare kuma komai nasu na kowanensu ne,

Read Ayyukan Manzanni 2Ayyukan Manzanni 2
Compare Ayyukan Manzanni 2:10-44Ayyukan Manzanni 2:10-44