Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 28

Ayyukan Manzanni 28:9-24

Help us?
Click on verse(s) to share them!
9Sa'adda wannan ya faru, sauran marasa lafiya da ke tsibirin sun zo sun sami warkarwa.
10Mutanen sun mutunta mu kwarai. Yayin da muke shirin tafiya, sun bamu duk abinda muke bukata.
11Bayan watanni uku, mun shiga jirgin Iskandariya wanda tun da hunturu yake a tsibirin mai zane kamannin Tagwaye Maza.
12Bayan saukar mu a birnin Sirakus, mun yi kwana uku a wurin.
13Daga nan sai muka tafi, har muka zo birnin Rigiyum. Bayan kwana daya iska mai karfi daga kudu ta taso, a cikin kwana biyu muka iso Butiyoli.
14A can muka iske wasu 'yan'uwa suka roke mu mu zauna tare da su har kwana bakwai. Ta wannan hanyar ce muka zo Roma.
15Daga can da 'yan'uwa suka ji labarin mu, suka fito don su tarbe mu tun daga Kasuwar Abiyas da kuma Rumfuna Uku. Da Bulus ya gan su, ya yi wa Allah godiya ya kuma sami karfafawa.
16Sa'adda muka shiga Roma, aka yardar wa Bulus ya zauna shi kadai tare da sojan da ke tsaronsa.
17Ana nan bayan kwana uku, Bulus ya kira shugabannin Yahudawa. Bayan da suka taru, sai ya ce masu, “Yan'uwa, ko da shike ban yi wa kowa laifi ko keta al'adun Ubanninmu ba, duk da haka an bashe ni daurarre tun daga Urushalima zuwa ga hannunwan mutanen Roma.
18Bayan tuhumata, sun yi kudirin saki na, domin ban yi laifin da ya cancanci mutuwa ba.
19Amma da Yahudawa suka tsaya a kan ra'ayin su, ya zama dole in daukaka kara zuwa ga Kaisar, ba domin ina da wani dalilin da zan yi karar al'ummata ba ne.
20Saboda wannan ne na bukaci ganinku in yi magana da ku. Saboda begen da Isra'ila suke da shi ya sa nake daure da wannan sarkar”.
21Sai suka ce masa, “Bamu karbi wasiku daga Yahudiya game da kai ba, babu kuma wani daga cikin 'yan'uwa wanda ya kawo mana wani rahoto ko wata magana game da kai.
22Amma muna so mu ji daga gare ka abin da kayi tunani ka kuma gani game da wannan darikar, gama mun sani ana kushenta a ko'ina.”
23Sa'adda suka sa masa rana, mutane da dama suka same shi a masaukinsa. Ya gabatarda zantattukan a gare su, yana tabbatar da bayyanuwar mulkin Allah. Har ya nemi ya rinjaye su a kan zancen Yesu, tun daga attaurat ta Musa zuwa litattafan annabawa, ya yi wannan tun daga safiya har yamma.
24Wasu sun kawar da shakkar abin da aka fada, amma wadansu basu gaskanta ba.

Read Ayyukan Manzanni 28Ayyukan Manzanni 28
Compare Ayyukan Manzanni 28:9-24Ayyukan Manzanni 28:9-24