Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 28

Ayyukan Manzanni 28:6-19

Help us?
Click on verse(s) to share them!
6Sun saurara su gani ko zai kumbura ko ya fadi matacce. Amma da suka jira dan lokaci basu ga wata matsala ta same shi ba sai suka canza tunaninsu sukace shi wani allah ne.
7A kusa da wannan wurin tsibirin akwai wasu gonakin wani babban mutumin tsibirin, mai suna Babiliyas. Ya karbe mu ya biya bukatun mu har kwana uku.
8Ana nan ashe mahaifin Babiliyas yana fama da zazzabi da atuni. Bulus ya shiga, yayi masa addu'a, ya dibiya masa hannu, ya sami warkarwa.
9Sa'adda wannan ya faru, sauran marasa lafiya da ke tsibirin sun zo sun sami warkarwa.
10Mutanen sun mutunta mu kwarai. Yayin da muke shirin tafiya, sun bamu duk abinda muke bukata.
11Bayan watanni uku, mun shiga jirgin Iskandariya wanda tun da hunturu yake a tsibirin mai zane kamannin Tagwaye Maza.
12Bayan saukar mu a birnin Sirakus, mun yi kwana uku a wurin.
13Daga nan sai muka tafi, har muka zo birnin Rigiyum. Bayan kwana daya iska mai karfi daga kudu ta taso, a cikin kwana biyu muka iso Butiyoli.
14A can muka iske wasu 'yan'uwa suka roke mu mu zauna tare da su har kwana bakwai. Ta wannan hanyar ce muka zo Roma.
15Daga can da 'yan'uwa suka ji labarin mu, suka fito don su tarbe mu tun daga Kasuwar Abiyas da kuma Rumfuna Uku. Da Bulus ya gan su, ya yi wa Allah godiya ya kuma sami karfafawa.
16Sa'adda muka shiga Roma, aka yardar wa Bulus ya zauna shi kadai tare da sojan da ke tsaronsa.
17Ana nan bayan kwana uku, Bulus ya kira shugabannin Yahudawa. Bayan da suka taru, sai ya ce masu, “Yan'uwa, ko da shike ban yi wa kowa laifi ko keta al'adun Ubanninmu ba, duk da haka an bashe ni daurarre tun daga Urushalima zuwa ga hannunwan mutanen Roma.
18Bayan tuhumata, sun yi kudirin saki na, domin ban yi laifin da ya cancanci mutuwa ba.
19Amma da Yahudawa suka tsaya a kan ra'ayin su, ya zama dole in daukaka kara zuwa ga Kaisar, ba domin ina da wani dalilin da zan yi karar al'ummata ba ne.

Read Ayyukan Manzanni 28Ayyukan Manzanni 28
Compare Ayyukan Manzanni 28:6-19Ayyukan Manzanni 28:6-19