Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 27

Ayyukan Manzanni 27:3-21

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Washegari muka sauka birnin Sidon, inda Yuliyas ya nuna wa Bulus karamci ya kuma yarda abokansa su bi shi don ya kula da su.
4Daga wurin, muka bi teku muka tafi ta Tsibirin Kubrus, domin matsananciyar iska da ke gaba damu.
5Sa'adda muka ketare ruwa zuwa sassan Kilikiya da Bamfiliya, muka zo Mira ta birnin Lisiya.
6Anan, jarumin ya sami jirgin ruwa daga Iskandariya wanda za shi Italiya. Ya samu cikinsa.
7Kwana da kwanaki muna tafiya a hankali a karshe da kyar muka sauka kusa da Sinidus, iska ta hana mu tafiya, sai muka ratsa ta Karita, kusa da Salmina.
8Da wahala muka bi ta makurda har muka zo wani wuri da ake kira Mafaka Mai Kyau wanda ke kusa da birnin Lasiya.
9Yanzu mun dauki dogon lokaci, gashi lokacin azumin Yahudawa ya wuce, tafiyar kuma ta zama da hatsari. Bulus ya gargade su,
10ya ce, “Jama'a, na gane tafiyarmu zata zamar mana da barna da asara mai yawa, ba ga kaya da jirgin kadai ba amma har da rayukan mu.”
11Amma jarumin ya fi mai da hankali ga maganar shugabansa da mai jirgin ruwan, fiye da abubuwan da Bulus ya fadi.
12Da shike tashar ba za ta yi dadin zama da hunturu ba, mafi yawa sun ba da shawara a bar wurin, in maiyiwuwa ne muga mun kai birnin Finikiya, don mu yi hunturu a can. Finikiya tashar jirgin ruwa ce a Karita, tana fuskantar arewa maso gabas da kudu maso gabas.
13Sa'adda iska daga kudu ta huro a hankali, sun tsammaci bukatarsu ta biya. Sai suka janye linzamin jirgin ruwan sukabi ta Karita kusa da gaba.
14Amma bayan wani dan lokaci sai iska mai karfi da ake kira Yurokilidon, ta fara bugun mu daga tsibirin.
15Sa'adda Jirgin ruwan ya kasa fuskantar iskar, sai muka bi inda iskar ta nufa.
16Sai muka bi ta inda muka sami kariya kusa da wani dan tsibiri wanda ake kira Kauda; kuma da wahala muka daure karamin jirgin a jikin babban.
17Bayanda suka daga shi, sun yi amfani da igiyoyi don su daure jirgin don gudun fadawa kan yashin Sirtis, suka bar jirgin yana ta korarsu.
18Mun yi ta fama da hadari ba kadan ba, da gari ya waye ma'aikatan jirgin suka fara zubar da kaya daga jirgin.
19A rana ta uku, ma'aikatan jirgi suka jefar da kaya daga cikin jirgin da hannuwansu.
20Kwanaki dayawa ba mu ga hasken rana da taurari a bisan mu ba. Babban hadari kadai ke dukanmu, duk mun fidda zuciya zamu tsira.
21Sa'adda sun dade basu ci abinci ba, sai Bulus ya tashi a gaban ma'aikatan jirgi yace, “Jama'a, da kun saurare ni, da bamu tashi daga Karita ba, balle mu fuskanci wannan barna da asarar.

Read Ayyukan Manzanni 27Ayyukan Manzanni 27
Compare Ayyukan Manzanni 27:3-21Ayyukan Manzanni 27:3-21