Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 27

Ayyukan Manzanni 27:1-14

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Bayan da aka amince zamu tafi Italiya, sun mika Bulus tare da wadansu daurarru a hanun wani jarumi mai suna Yuliyas, daga batalian Agustas.
2Muka shiga Jirgin ruwa daga Adramatiya, wanda ke shirin tashi zuwa kusa da gefen tekun Asiya. Sai muka je teku. Aristakus mutumin Tasalonika a Makidoniya ya tafi tare damu.
3Washegari muka sauka birnin Sidon, inda Yuliyas ya nuna wa Bulus karamci ya kuma yarda abokansa su bi shi don ya kula da su.
4Daga wurin, muka bi teku muka tafi ta Tsibirin Kubrus, domin matsananciyar iska da ke gaba damu.
5Sa'adda muka ketare ruwa zuwa sassan Kilikiya da Bamfiliya, muka zo Mira ta birnin Lisiya.
6Anan, jarumin ya sami jirgin ruwa daga Iskandariya wanda za shi Italiya. Ya samu cikinsa.
7Kwana da kwanaki muna tafiya a hankali a karshe da kyar muka sauka kusa da Sinidus, iska ta hana mu tafiya, sai muka ratsa ta Karita, kusa da Salmina.
8Da wahala muka bi ta makurda har muka zo wani wuri da ake kira Mafaka Mai Kyau wanda ke kusa da birnin Lasiya.
9Yanzu mun dauki dogon lokaci, gashi lokacin azumin Yahudawa ya wuce, tafiyar kuma ta zama da hatsari. Bulus ya gargade su,
10ya ce, “Jama'a, na gane tafiyarmu zata zamar mana da barna da asara mai yawa, ba ga kaya da jirgin kadai ba amma har da rayukan mu.”
11Amma jarumin ya fi mai da hankali ga maganar shugabansa da mai jirgin ruwan, fiye da abubuwan da Bulus ya fadi.
12Da shike tashar ba za ta yi dadin zama da hunturu ba, mafi yawa sun ba da shawara a bar wurin, in maiyiwuwa ne muga mun kai birnin Finikiya, don mu yi hunturu a can. Finikiya tashar jirgin ruwa ce a Karita, tana fuskantar arewa maso gabas da kudu maso gabas.
13Sa'adda iska daga kudu ta huro a hankali, sun tsammaci bukatarsu ta biya. Sai suka janye linzamin jirgin ruwan sukabi ta Karita kusa da gaba.
14Amma bayan wani dan lokaci sai iska mai karfi da ake kira Yurokilidon, ta fara bugun mu daga tsibirin.

Read Ayyukan Manzanni 27Ayyukan Manzanni 27
Compare Ayyukan Manzanni 27:1-14Ayyukan Manzanni 27:1-14