Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 25

Ayyukan Manzanni 25:11-19

Help us?
Click on verse(s) to share them!
11Idan lallai na yi laifi kuma na yi abin da ya chanchanci mutuwa, ban ki ba in mutu. Amma idan zarginsu karya ne, kada kowa ya bashe ni gare su. Ina daukaka kara zuwa ga Kaisar.”
12Bayan Festas ya tattauna da majalisa ya amsa ya ce, “Kana kira ga Kaisar; za ka tafi wurin Kaisar.”
13Bayan wadansu kwanaki, sarki Agaribas da Barniki suka iso Kaisariya domin su ziyarci Festas.
14Da ya kasance kwanaki da yawa, Festas ya fada wa sarki labarin Bulus ya ce, “Akwai wani mutum dan sarka da Filikus ya bari a kurkuku.
15Sa'anda nake a Urushalima, babban firist da dattawan Yahudawa suka kawo kararsa gare ni, suka roka a kashe shi.
16Game da wannan na amsa na ce masu, ba al'adar Romawa ba ce a ba da mutum tagomashi; sai wanda ake kararsa an bashi zarafi ya kare kansa a gaban masu kararsa, ya kuma bada hujjojinsa game da kararakin.
17Saboda haka, da duk suka taru ban bata lokaci ba, washegari na zauna a kujerar shari'a, na ba da umarni a kawo mutumin.
18Da masu karar suka fadi kararsu, sai na fahimci karar ba wani muhimmin abu a cikinta.
19Sai dai na ga cewa jayayya ce tsakanin su ta addini a kan wani Yesu da ya mutu, wanda Bulus ya ce yana da rai.

Read Ayyukan Manzanni 25Ayyukan Manzanni 25
Compare Ayyukan Manzanni 25:11-19Ayyukan Manzanni 25:11-19