Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 23

Ayyukan Manzanni 23:7-28

Help us?
Click on verse(s) to share them!
7Daya fadi haka, mahawara ta fara a tsakanin Farisawa da Sadukiyawa, sai taron ya rabu kashi biyu.
8Don Sadukiyawa suka ce babu tashin matattu, babu mala'iku, babu kuma ruhohi, amma Farisawa suka ce dukan abubuwan nan sun kasance.
9Sai mahawara ta tashi, wadansu marubutan Farisawa suka tashi da mahawara cewa, “Ba mu same mutumin nan da laifi ba sam. Ko mala'iku da ruhohi ne suka yi masa magana?”
10Da jayayya ta tashi, babban hafsa ya ji tsoro kada su yayaga Bulus, sai ya umarce sojoji suje su kwato shi da karfi daga 'yan majalisa, su tafi da shi farfajiya.
11Da dare Ubangiji ya tsaya kusa da shi yace, “Kada ka ji tsoro, kamar yadda ka ba da shaida game da ni a Urushalima, dole zaka sake zama shaida a Roma.”
12Da gari ya waye, wadansu Yahudawa sun yi yarjejeniya suka dauka wa kansu la'ana: suka ce ba za su ci ba ba za su sha ba sai sun kashe Bulus.
13Mutane fiye da arba'in suka kulla wannan makirci.
14Suka je wurin manyan firistoci da dattawa suka ce, “Mun sa wa kanmu la'ana, ba za mu ci ba, ba za mu sha ba sai mun kashe Bulus.
15Yanzu, bari majalisa ta ba wa babban hafsa izini a kawo shi a gaba, kamar zai yanke hukunci. Mu kam, a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso nan.
16Amma dan yar'uwan Bulus ya ji suna labe, sai ya tafi ya shiga farfajiyar ya fada wa Bulus.
17Bulus ya kira daya daga cikin jarumai yace, “Dauki saurayin nan ka kai shi wurin babban hafsa, don yana da abin da zai fada masa.”
18Jarumin ya dauke saurayin ya kai shi wurin babban hafsa yace, “Bulus dan sarka ne yace in kawo saurayin nan a gaban ka. Yana da abin da zai fada maka.”
19Babban hafsa ya kai shi wani lungu, sai ya tambaye shi, “Menene kake so ka fada mani?”
20Saurayin yace, “Yahudawa sun yarda su roke ka ka kawo Bulus gobe a majalisa, kamar zasu kara bincike a kan al'amarin.
21Amma kada ka yarda da su, mutane fiye da arba'in suna jiransa. Sun sa wa kansu la'anna, ba za su ci ba ba za su sha ba sai dai sun kashe shi. Yanzu a shirye suke; suna jira ka ba su izini.”
22Sai babban hafsa yace wa saurayin ya tafi, da ya gama masa magana, “Kar ka fada wa wani al'amuran.”
23Sai ya kira jarumai biyu yace, “Ku shirya sojoji dari biyu, yan dawakai saba'in, masu daukar mashi dari biyu su tafi kaisariya karfe uku na dare.”
24Ya umarta a shirya dabbobin da Bulus zai hawo da zasu kai shi lafiya wurin Filikus gwamna.
25Sai ya rubuta wasika a misalin haka:
26Gaisuwa zuwa Kuludiyas Lisiyas zuwa ga mai martaba gwamna Filikus.
27Yahudawa sun kama wannan mutumin suna shirin kashe shi, na abko masu da sojoji na kwace shi, bayan da na ji shi Barome ne.
28Inna son sani dalilin zarginsa, sai na kai shi majalisa.

Read Ayyukan Manzanni 23Ayyukan Manzanni 23
Compare Ayyukan Manzanni 23:7-28Ayyukan Manzanni 23:7-28