Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 23

Ayyukan Manzanni 23:15-24

Help us?
Click on verse(s) to share them!
15Yanzu, bari majalisa ta ba wa babban hafsa izini a kawo shi a gaba, kamar zai yanke hukunci. Mu kam, a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso nan.
16Amma dan yar'uwan Bulus ya ji suna labe, sai ya tafi ya shiga farfajiyar ya fada wa Bulus.
17Bulus ya kira daya daga cikin jarumai yace, “Dauki saurayin nan ka kai shi wurin babban hafsa, don yana da abin da zai fada masa.”
18Jarumin ya dauke saurayin ya kai shi wurin babban hafsa yace, “Bulus dan sarka ne yace in kawo saurayin nan a gaban ka. Yana da abin da zai fada maka.”
19Babban hafsa ya kai shi wani lungu, sai ya tambaye shi, “Menene kake so ka fada mani?”
20Saurayin yace, “Yahudawa sun yarda su roke ka ka kawo Bulus gobe a majalisa, kamar zasu kara bincike a kan al'amarin.
21Amma kada ka yarda da su, mutane fiye da arba'in suna jiransa. Sun sa wa kansu la'anna, ba za su ci ba ba za su sha ba sai dai sun kashe shi. Yanzu a shirye suke; suna jira ka ba su izini.”
22Sai babban hafsa yace wa saurayin ya tafi, da ya gama masa magana, “Kar ka fada wa wani al'amuran.”
23Sai ya kira jarumai biyu yace, “Ku shirya sojoji dari biyu, yan dawakai saba'in, masu daukar mashi dari biyu su tafi kaisariya karfe uku na dare.”
24Ya umarta a shirya dabbobin da Bulus zai hawo da zasu kai shi lafiya wurin Filikus gwamna.

Read Ayyukan Manzanni 23Ayyukan Manzanni 23
Compare Ayyukan Manzanni 23:15-24Ayyukan Manzanni 23:15-24