Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 20

Ayyukan Manzanni 20:6-28

Help us?
Click on verse(s) to share them!
6Da muka shiga Jirgi daga Filibi bayan kwanakin Gurasa mara yisti; bayan kwanaki biyar muka iske su a Taruwasa; kwananmu bakwai a wurin.
7A rana ta fari ga mako, da muka taru domin karya gurasa. Bulus ya yi wa masubi jawabi, don ya yi niyyar ya tafi da wayewar gari; jawabinsa ya kai har tsakar dare.
8A benen da suka taru akwai fitilu da yawa.
9Wani matashi mai suna Aftikos yana zaune a kan taga, barci mai nauyi ya dauke shi; da shike Bulus ya tsawaita jawabinsa, saurayin da shike barci mai nauyi ya dauke shi sai ya fado daga kan bene na uku aka dauke shi matacce.
10Sai Bulus ya sauka ya mike a bisansa ya rungume shi, sa'annan ya ce, “Kada kowa ya damu; domin yana darai bai mutu ba.”
11Sa'annan ya hawo kan bene domin cin gurasa tare da su, ya yi magana da su har gari ya waye daga nan ya bar su.
12Suka kawo saurayin da rai, sun sami ta'aziya ba kadan ba.
13Amma mu, da muka riga Bulus zuwa gun Jirgin, muka shiga zuwa Asos, mun shirya mu dauki Bulus a jirgi amma shi ya kudurta ya yi tafiya a kasa.
14Da muka sadu a Asos, mun dauke shi a Jirgin ruwa zuwa Mitilitus.
15Bayan tashin mu daga can, washegari muka zo tsibirin Kiyos. Washegari kuma muka zo birnin Militus.
16Amma Bulus ya kudurta wucewa Afisa a Jirgi, don kada ya bata lokaci a Asiya, don yana sauri in ya yiwu ranar Fentekos ta same shi a Urushalima.
17Daga Militus ya aika a kira masa dattawan iklisiyar Afisa.
18Da suka zo wurinsa sai ya ce masu, “Ku da kanku kun san tun daga ranar da na sa kafata a Asiya, irin zaman da muka yi da kasancewar mu tare.
19Na bauta wa Ubangiji da tawaliu har da hawaye, da wahalun da na sha saboda makircin Yahudawa.
20Kun sani ban ji nauyin sanar da ku kowanne abu mai amfani ba, na bi ku gida gida ina koyar da ku abubuwa a sarari.
21Kunsan yadda na gargadi Yahudawa da Hellenawa game da tuba ga Allah da bangaskiya ga Ubangiji Yesu.
22Yanzu fa, gashi, zan tafi Urushalima, Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a fili dole in je, ban san abin da zai faru da ni a can ba.
23Sai dai Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a kowanne gari cewa, sarkoki da wahalu suna jira na.
24Amma ban dauka cewa raina yana da wani amfani gare ni ba, domin in cika tsere da hidimar da na karba daga wurin Ubangiji Yesu, ta shaidar bisharan alherin Allah.
25Yanzu fa, duba, na san dukanku, wadanda na yi wa wa'azin mulkin Allah, ba za ku kara gani na ba.
26Don haka na shaida maku a wannan rana, ba ni da alhakin jinin kowanne mutum.
27Don banji nauyin sanar maku da dukan nufin Allah a gare ku ba.
28Saboda haka ku kula da kanku, da masubi da Ruhu Mai Tsarki ya sanya ku shugabanni. Ku kula ku yi kiwon iklisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.

Read Ayyukan Manzanni 20Ayyukan Manzanni 20
Compare Ayyukan Manzanni 20:6-28Ayyukan Manzanni 20:6-28