Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 20

Ayyukan Manzanni 20:30-34

Help us?
Click on verse(s) to share them!
30Na sani har daga cikinku wadansu mazaje za su zo su fadi gurbattatun zantattuka, domin su janye almajirai zuwa gare su.
31Saboda haka ku yi lura. Ku tuna da cewa shekara uku ban fasa yi wa kowannenku gargadi da hawaye dare da rana ba.
32Yanzu ina mika ku ga Allah, da maganar Alherinsa, wadda take da ikon gina ku ta kuma ba ku gado tare da dukan wadanda ke cikin kebabbu na Allah.
33Ban yi kyashin azurfa, ko zinariya, ko tufafin wani ba.
34Ku da kanku kun sani na yi aiki da hannuwana, na biya bukatu na da na wadanda ke tare da ni.

Read Ayyukan Manzanni 20Ayyukan Manzanni 20
Compare Ayyukan Manzanni 20:30-34Ayyukan Manzanni 20:30-34