Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 20

Ayyukan Manzanni 20:23-32

Help us?
Click on verse(s) to share them!
23Sai dai Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a kowanne gari cewa, sarkoki da wahalu suna jira na.
24Amma ban dauka cewa raina yana da wani amfani gare ni ba, domin in cika tsere da hidimar da na karba daga wurin Ubangiji Yesu, ta shaidar bisharan alherin Allah.
25Yanzu fa, duba, na san dukanku, wadanda na yi wa wa'azin mulkin Allah, ba za ku kara gani na ba.
26Don haka na shaida maku a wannan rana, ba ni da alhakin jinin kowanne mutum.
27Don banji nauyin sanar maku da dukan nufin Allah a gare ku ba.
28Saboda haka ku kula da kanku, da masubi da Ruhu Mai Tsarki ya sanya ku shugabanni. Ku kula ku yi kiwon iklisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.
29Na sani cewa bayan tafiyata, kyarketai masu zafi za su shiga tsakaninku, kuma baza su rangwanta wa masubi ba.
30Na sani har daga cikinku wadansu mazaje za su zo su fadi gurbattatun zantattuka, domin su janye almajirai zuwa gare su.
31Saboda haka ku yi lura. Ku tuna da cewa shekara uku ban fasa yi wa kowannenku gargadi da hawaye dare da rana ba.
32Yanzu ina mika ku ga Allah, da maganar Alherinsa, wadda take da ikon gina ku ta kuma ba ku gado tare da dukan wadanda ke cikin kebabbu na Allah.

Read Ayyukan Manzanni 20Ayyukan Manzanni 20
Compare Ayyukan Manzanni 20:23-32Ayyukan Manzanni 20:23-32