Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 1

Ayyukan Manzanni 1:3-11

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Bayan ya sha wahala, ya bayyana kan sa da rai a garesu, da alamu da dama masu gamsarwa. Kwana arba'in ya baiyana kansa a garesu yana yi masu magana game da mulkin Allah.
4Yayin da yana zaune tare da su ya basu umarni cewa kada su bar Urushalima, amma su jira alkawarin Uban, wanda ya ce, “Kun ji daga gare ni,
5cewa Yahaya babu shakka ya yi baftisma da ruwa, amma ku za a yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki nan da kwanaki kadan.”
6Sa'adda suna tare suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci ne za ka maido da mulki ga Isra'ila?”
7Ya ce masu, “Ba naku bane ku san lokaci ko sa'a wanda Uba ya shirya ta wurin ikonsa.
8Amma za ku karbi iko, idan Ruhu Mai Tsarki ya zo bisanku, sa'annan za ku zama shaidu na cikin Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, har ya zuwa karshen duniya.”
9Lokacin da Ubangiji Yesu ya fadi wadannan abubuwa, yayin da suna kallon sama, sai aka dauke shi zuwa sama, kuma girgije ya boye shi daga idanunsu.
10Da suka dinga kallon sama yayin da ya tafi, nan da nan, mazaje biyu suka tsaya a gabansu cikin fararen tufafi.
11Suka ce, “Ku mazajen Galili me yasa ku ke tsaye a nan kuna kallon sama? Wannan Yesu wanda ya hau zuwa sama zai dawo kamar yadda kuka gan shi yana tafiya zuwa sama.”

Read Ayyukan Manzanni 1Ayyukan Manzanni 1
Compare Ayyukan Manzanni 1:3-11Ayyukan Manzanni 1:3-11