Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 19

Ayyukan Manzanni 19:8-18

Help us?
Click on verse(s) to share them!
8Bulus ya shiga majami'a ya yi ta koyarwa gabagadi misalin tsawon wata uku. Yana bi da su cikin nazarin maganar yana fahimtar da mutane su gaskanta game da abubuwa da suka shafi mulkin Allah.
9Amma sa'adda wadansu Yahudawa suka taurare, suka ki yin biyayya, sai suka fara bata hanyar Almasihu a gaban taron. Saboda haka sai Bulus ya janye daga wurinsu tare da wadanda suka ba da gaskiya. Ya fara koyarwa a makarantar Tiranus.
10Haka ya cigaba shekaru biyu har duk mazaunan Asiya suka ji maganar Ubangiji, Yahudawa da Helenawa.
11Allah ya yi manyan al'ajibai ta hannun Bulus,
12har marasa lafiya suka warke, mugayen ruhohi suka fito daga cikin mutane, sa'adda suka karbi kyallaye da mayafai daga jikin Bulus.
13Amma akwai Yahudawa masu tsubu da suka biyo ta wajen, suka dauka wa kansu su yi amfani da sunan Yesu. Suka ce, “Mun dokace ku cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa'azinsa, ku fita.”
14Wadanda suka yi wannan su bakwai ne 'ya'yan wani babban firist Bayahude mai suna Siba.
15Mugun ruhun ya amsa ya ce, “Na san Yesu, na san Bulus, amma ku, su wanene?”
16Sai mugun ruhun da ke cikin mutumin ya fada a kan matsubatan ya fi karfinsu ya kuma bubuge su. Suka runtuma da gudu suka fice daga dakin tsirara da raunuka.
17Wannan ya zama sanannen abu ga dukan mutane, Yahudawa da Helenawa mazaunan Afisa. Suka ji tsoro kwarai, sunan Ubangiji Yesu ya sami daukaka.
18Masu bi da yawa kuma, suka zo suka furta mugayen ayyukan da suka aikata.

Read Ayyukan Manzanni 19Ayyukan Manzanni 19
Compare Ayyukan Manzanni 19:8-18Ayyukan Manzanni 19:8-18