Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 19

Ayyukan Manzanni 19:22-36

Help us?
Click on verse(s) to share them!
22Bulus ya aiki almajiransa biyu Timoti da Irastus zuwa Makidoniya, wadanda suka taimake shi. Amma shi da kansa ya jira a Asiya na dan lokaci.
23A wannan lokacin sai aka yi babban tashin hankali a Afisa game da wannan Hanyar.
24Wani Makeri mai suna Damatrayus wanda ke kera sifoffin gunkin azurfa na Dayana, wanda sana'a ce mai kawo wa makera riba sosai.
25Ya tattara makera ya ce da su, “Kun sa ni da wanan sana'a ne muke samun kudi mai yawa.
26Kun gani kun kuma ji cewa, ba a Afisa kadai ba, amma har da fadin kasar Asiya wannan Bulus ya rinjayi mutane da yawa. Yana cewa babu alloli da ake kerawa da hannu.
27Ba sana'ar mu kadai ke cikin hatsari ba, amma har da haikalin allahnmu Dayana babba zai zama mara amfani. Ta haka za ta rasa girmanta, ita da dukan kasar Asiya da duniya ke wa sujada.”
28Da suka ji haka sai suka fusata kwarai, suka yi kira mai karfi suna cewa “Mai girma ce Dayana ta Afisa.”
29Gari gaba daya ya rude, jama'a kuma sun hanzarta zuwa wurin taron. Kafin wannan lokaci, sun riga sun kama abokan tafiyar Bulus, wato Gayus da Aristakas wadanda suka zo daga Makidoniya.
30Bulus ya yi niyya ya shiga cikin taron jama'ar, amma almajiran suka hana shi.
31Haka nan ma wadansu abokan Bulus da ke shugabanin yankin al'umma Asiya sun aika masa da roko mai karfi kada ya shiga dandalin.
32Wadansu mutane na kirarin wani abu, wadansu kuma na kirarin wani abu dabam, domin jama'a sun rude. Da yawa daga cikinsu ma ba su san dalilin taruwarsu ba.
33Yahudawa suka kawo Iskandari ya tsaya a gaban taruwan jama'a. Iskandari ya mika hannunsa sama domin ya yi bayani ga jama'a.
34Amma da suka gane shi Bayahude ne, sai dukansu suka kwala ihu wajen sa'a biyu, “Mai girma ce Dayana ta Afisa.”
35Da magatakardar garin ya sha kan jama'a, sai ya ce, “Ya ku mutanen Afisa, wanene bai san cewa birnin Afisa cibiya ce na allahn nan Dayana mai girma da na sifar da ta fado daga sama ba?
36Tun da ba a karyata wadannan abubuwa ba, ya kamata ku yi shuru don kada ku yi wani abu a gaggauce.

Read Ayyukan Manzanni 19Ayyukan Manzanni 19
Compare Ayyukan Manzanni 19:22-36Ayyukan Manzanni 19:22-36