Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 18

Ayyukan Manzanni 18:6-23

Help us?
Click on verse(s) to share them!
6Lokacin da Yahudawa suka tayar masa suna zarginsa. Bulus ya kakkabe rigansa a gabansu yana cewa, “Alhakin jininku yana kanku; daga yanzu zan koma wurin al'ummai.”
7Da ya bar wurinsu, ya tafi gidan Taitus Yustus mai wa Allah sujada. Gidansa na kusa da majami'a.
8Kiristus shine shugaban majami'a, sai shi da dukan iyalin gidansa sun ba da gaskiya ga Ubangiji. Korantiyawa da yawa suka ji jawabin Bulus suka ba da gaskiya, aka yi masu Baftisma.
9Da dare Ubangiji ya ce wa Bulus a cikin wahayi, “Kada ka ji tsoro, amma ka yi magana kada kuma ka yi shuru.
10Gama ina tare da kai, ba wanda zai cutar da kai, gama ina da mutane anan garin.”
11Bulus ya zauna a nan tsawon shekara daya da wata shida, yana koyar masu da maganar Allah.
12Amma da Galiyo ya samu zaman gwamnan Akaya, sai Yahudawa suka tayar wa Bulus har suka kai shi gaban dakalin shari'a.
13Suna cewa, “Wannan mutumin yana kokarin rinjayar mutane su yi sujadar da ta saba wa dokarmu.”
14Duk da haka kafin Bulus ya yi magana, Galiyo ya ce wa Yahudawa, “Ku Yahudawa in da karar ku ta wani babban laifi ce wanda ya aikata, da sai in hukunta.
15Amma tun da ya ke akan al'amurar, kalmomi ne, da ta sunaye da dokokin ku, ku je ku sasanta al'amuran ku.”
16Galiyo ya kore su daga dakalin shari'a.
17Saboda haka sai suka kama Sastanisu, suka yi masa duka sosai a gaban dakalin shari'a. Amma Galiyo bai damu da yadda suka karasa ba.
18Bulus kuwa, bayan ya zauna tare da su na wasu kwanaki masu yawa, ya bar 'yan'uwan zuwa Suriya ta jirgin ruwa, tare da Balkisu da Akila. Kafin ya bar tashar jiragen ruwa da ke a Sankuriya, ya tafi saboda ya aske kansa, domin ya dauki alkawarin Banazare.
19Da suka iso Afisa, Bulus ya bar Balkisu da Akila anan. Shi kuwa ya shiga majami'ar Yahudawa yana nazari tare da su.
20Da suka roki Bulus ya zauna da su na tsawon lokaci, bai yarda ba.
21Ya kama hanyarsa ya bar su ya ce, “In Allah ya yardar mani zan dawo wurinku wata rana.” Sai ya shiga jirgin ruwa daga Afisa.
22Daga saukar su a Kaisariya, sai ya haura zuwa Urushalima ya gai da iklisiya daga nan ya tafi Antakiya.
23Bayan ya zauna na dan lokaci a wurin, Bulus ya kama hanyarsa zuwa yakin Galatiya da Firjiya anan ya karfafa almajirai.

Read Ayyukan Manzanni 18Ayyukan Manzanni 18
Compare Ayyukan Manzanni 18:6-23Ayyukan Manzanni 18:6-23