Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 18

Ayyukan Manzanni 18:4-8

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Saboda haka Bulus na zuwa majami'a, yana yin nazari tare da su a kowace Asabaci. Yana kokari ya rinjayi Yahudawa da Helinawa.
5Amma a lokacin da Sila da Timoti suka iso Makidoniya, Ruhu ya matsa Bulus ya shaida wa Yahudawa cewa Yesu Almasihu ne.
6Lokacin da Yahudawa suka tayar masa suna zarginsa. Bulus ya kakkabe rigansa a gabansu yana cewa, “Alhakin jininku yana kanku; daga yanzu zan koma wurin al'ummai.”
7Da ya bar wurinsu, ya tafi gidan Taitus Yustus mai wa Allah sujada. Gidansa na kusa da majami'a.
8Kiristus shine shugaban majami'a, sai shi da dukan iyalin gidansa sun ba da gaskiya ga Ubangiji. Korantiyawa da yawa suka ji jawabin Bulus suka ba da gaskiya, aka yi masu Baftisma.

Read Ayyukan Manzanni 18Ayyukan Manzanni 18
Compare Ayyukan Manzanni 18:4-8Ayyukan Manzanni 18:4-8