Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 18

Ayyukan Manzanni 18:11-28

Help us?
Click on verse(s) to share them!
11Bulus ya zauna a nan tsawon shekara daya da wata shida, yana koyar masu da maganar Allah.
12Amma da Galiyo ya samu zaman gwamnan Akaya, sai Yahudawa suka tayar wa Bulus har suka kai shi gaban dakalin shari'a.
13Suna cewa, “Wannan mutumin yana kokarin rinjayar mutane su yi sujadar da ta saba wa dokarmu.”
14Duk da haka kafin Bulus ya yi magana, Galiyo ya ce wa Yahudawa, “Ku Yahudawa in da karar ku ta wani babban laifi ce wanda ya aikata, da sai in hukunta.
15Amma tun da ya ke akan al'amurar, kalmomi ne, da ta sunaye da dokokin ku, ku je ku sasanta al'amuran ku.”
16Galiyo ya kore su daga dakalin shari'a.
17Saboda haka sai suka kama Sastanisu, suka yi masa duka sosai a gaban dakalin shari'a. Amma Galiyo bai damu da yadda suka karasa ba.
18Bulus kuwa, bayan ya zauna tare da su na wasu kwanaki masu yawa, ya bar 'yan'uwan zuwa Suriya ta jirgin ruwa, tare da Balkisu da Akila. Kafin ya bar tashar jiragen ruwa da ke a Sankuriya, ya tafi saboda ya aske kansa, domin ya dauki alkawarin Banazare.
19Da suka iso Afisa, Bulus ya bar Balkisu da Akila anan. Shi kuwa ya shiga majami'ar Yahudawa yana nazari tare da su.
20Da suka roki Bulus ya zauna da su na tsawon lokaci, bai yarda ba.
21Ya kama hanyarsa ya bar su ya ce, “In Allah ya yardar mani zan dawo wurinku wata rana.” Sai ya shiga jirgin ruwa daga Afisa.
22Daga saukar su a Kaisariya, sai ya haura zuwa Urushalima ya gai da iklisiya daga nan ya tafi Antakiya.
23Bayan ya zauna na dan lokaci a wurin, Bulus ya kama hanyarsa zuwa yakin Galatiya da Firjiya anan ya karfafa almajirai.
24A nan dai akwai wani Bayahude mai suna Afolos, dan asalin Iskandariya ne da haihuwa, ya zo Afisa. Shi masani ne a maganar Allah.
25Afolos dai ya sami horo daga maganar Ubangiji. Shi mai kokari ne a ruhu, yana wa'azi da koyarwa daidai game da Yesu. Amma ya san da Baftismar Yahaya ne kadai.
26Afolos ya fara wa'azinsa da gabagadi a cikin majami'a. Da Balkisu da Akila suka ji shi sai suka yi abokantaka da shi, suka kara bayyana masa game da labarin hanyar Allah mafi daidai.
27Da ya so ya wuce zuwa cikin Akaya 'yan'uwa suka karfafa shi, sun rubuta wa almajiran da ke a Akaya, don su karbe shi da hannu biyu. Da ya iso wurinsu, ya kuwa karfafa 'yan'uwa da sun ba da gaskiya ta wurin alheri.
28Afolos ya ba Yahudawa mamaki da irin ikon da yake da shi da gwanintarsa, yadda yake nunawa daga nassoshi cewa Yesu shine Almasihu.

Read Ayyukan Manzanni 18Ayyukan Manzanni 18
Compare Ayyukan Manzanni 18:11-28Ayyukan Manzanni 18:11-28