Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 18

Ayyukan Manzanni 18:1-13

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Bayan haka sai Bulus ya tafi Antakiya daga nan, ya wuce Korinti.
2A can ya sadu da wani Bayahude mai sunan Akila, dan kasar Buntus ne; bai dade da zuwa garin ba, daga Italiya ya zo da matarsa mai suna Balkisu, saboda Kalaudiyas ya ba da umarni dukan Yahudawa su bar Roma; sai Bulus ya je wurinsu.
3Bulus ya zauna a gidansu don sana'arsu daya ce, wato, masu aikin Tanti ne.
4Saboda haka Bulus na zuwa majami'a, yana yin nazari tare da su a kowace Asabaci. Yana kokari ya rinjayi Yahudawa da Helinawa.
5Amma a lokacin da Sila da Timoti suka iso Makidoniya, Ruhu ya matsa Bulus ya shaida wa Yahudawa cewa Yesu Almasihu ne.
6Lokacin da Yahudawa suka tayar masa suna zarginsa. Bulus ya kakkabe rigansa a gabansu yana cewa, “Alhakin jininku yana kanku; daga yanzu zan koma wurin al'ummai.”
7Da ya bar wurinsu, ya tafi gidan Taitus Yustus mai wa Allah sujada. Gidansa na kusa da majami'a.
8Kiristus shine shugaban majami'a, sai shi da dukan iyalin gidansa sun ba da gaskiya ga Ubangiji. Korantiyawa da yawa suka ji jawabin Bulus suka ba da gaskiya, aka yi masu Baftisma.
9Da dare Ubangiji ya ce wa Bulus a cikin wahayi, “Kada ka ji tsoro, amma ka yi magana kada kuma ka yi shuru.
10Gama ina tare da kai, ba wanda zai cutar da kai, gama ina da mutane anan garin.”
11Bulus ya zauna a nan tsawon shekara daya da wata shida, yana koyar masu da maganar Allah.
12Amma da Galiyo ya samu zaman gwamnan Akaya, sai Yahudawa suka tayar wa Bulus har suka kai shi gaban dakalin shari'a.
13Suna cewa, “Wannan mutumin yana kokarin rinjayar mutane su yi sujadar da ta saba wa dokarmu.”

Read Ayyukan Manzanni 18Ayyukan Manzanni 18
Compare Ayyukan Manzanni 18:1-13Ayyukan Manzanni 18:1-13