Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 17

Ayyukan Manzanni 17:9-23

Help us?
Click on verse(s) to share them!
9Bayan da sun amshi kudi daga wurin Yason da sauran 'yan'uwan, sai suka sake su.
10A wannan daren, 'yan'uwa masu bi suka fitar da Bulus da Sila, suka aike su garin Biriya. Da isar su can, su ka nufa majami'ar Yahudawa.
11Mutanen Biriya daban suke da na Tasalunika, sun yarda da sakon Bulus da zuciya daya, suna kuma binciken littattafai kowace rana domin su tabbatar da sakon Bulus, ko gaskiya ne.
12Saboda haka mutane da yawa cikin su sun ba da gaskiya, tare da wadansu sannanun mata Helenawa da maza da yawa.
13Amma da Yahudawan Tasalunika suka ji cewa Bulus yana wa'azin kalmar Allah a Biriya, sun haura can, sun tada hankulan jama'a.
14Nan da nan, masu bi na Biriya sun dauki Bulus sun aika shi zuwa teku, an bar Sila da Timoti a Biriya tukuna.
15Wadanda sun fitar da Bulus, sun kai shi har zuwa birnin Atina. Bulus ya ba su sako, su fada wa Sila da Timoti suyi hanzari su same shi.
16Sa'anda Bulus yana jiran zuwan Sila da Timoti a Atina, ya yi fushi a ransa, da ya ga birnin cike da gumakai.
17Ya tattauna da Yahudawa a cikin majami'a tare da masu yin sujada ga Allah, da kuma wadanda yake samu a kowace rana, a kasuwa.
18Amma wadan su Abikuriyawa da masana sun yi karo da shi. Wadansun su na cewa, “Menene wannan sakaren ke cewa?” Wadansu kuma sun ce, “Da alama mai wa'azi ne na wasu alloli dabam,” domin yana wa'azin Yesu da tashin sa daga matattu.
19Suka dauki Bulus zuwa Tudun Arasa, suna cewa, “Ko za ka sanar mana da wannan sabuwar koyaswar taka?
20Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma'anar su.”
21(Atiniyawa da bakin da ke cikinsu, suna ba da lokacin su ga fadin sabobbin abubuwa da sauraron su).
22Bulus ya tsaya a tsakiyar Tudun Arasa ya ce, “Ku mutanen Atiniya na lura masu kwazon addini ne ku.
23Na lura da abubuwan sujadar ku yayin da nake zagawa, amma na ga wani bagadi da rubutu a kansa mai cewa, “Ga Allah wanda ba a sani ba.” Abin da kuke bauta wa cikin rashin sani, shi nake sanar maku.

Read Ayyukan Manzanni 17Ayyukan Manzanni 17
Compare Ayyukan Manzanni 17:9-23Ayyukan Manzanni 17:9-23