Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 17

Ayyukan Manzanni 17:19-32

Help us?
Click on verse(s) to share them!
19Suka dauki Bulus zuwa Tudun Arasa, suna cewa, “Ko za ka sanar mana da wannan sabuwar koyaswar taka?
20Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma'anar su.”
21(Atiniyawa da bakin da ke cikinsu, suna ba da lokacin su ga fadin sabobbin abubuwa da sauraron su).
22Bulus ya tsaya a tsakiyar Tudun Arasa ya ce, “Ku mutanen Atiniya na lura masu kwazon addini ne ku.
23Na lura da abubuwan sujadar ku yayin da nake zagawa, amma na ga wani bagadi da rubutu a kansa mai cewa, “Ga Allah wanda ba a sani ba.” Abin da kuke bauta wa cikin rashin sani, shi nake sanar maku.
24Allahn da ya yi duniya da kome da ke cikinta, tun da ya ke shine Ubangijin sama da kasa, ba ya zama a haikalin da mutane suka gina da hannu.
25Ba ya neman taimakon kowa, babu kuma wanda ya isa ya ba shi. Shine ke ba da rai, da numfashi da kowanne abu.
26Daga mutum daya ya hallici dukan al'umman duniya, ya rarraba, ya kuma sanya kowa a inda ya shirya masa.
27Domin su nemi Allah ko za su iya kaiwa zuwa gareshi su same shi, ga shi kuwa ba ya nesa da kowannenmu.
28A cikinsa muke rayuwa, muna walwala, kamar yadda wani daga cikin masananku yace, 'Mu 'ya'yansa ne'.
29Idan mu 'ya'yan Allah ne, bai kamata mu danganta Allah da zinariya ko azurfa, ko kuma duwatsu da itatuwa da an sassaka ba.
30Saboda haka ne, Allah ya kawar da kwanakin jahilci, amma ya ba da umarni kowa a ko'ina ya tuba.
31Akwai ranar da ya shirya zai yi wa duniya shari'a cikin adalci, ta wurin mutumin da ya zaba. Allah ya nuna wannan mutumin, ta wurin ta da shi daga matattu”.
32Da mutanen Atina sun ji batun tashi daga matattu, wadansu suka yi wa Bulus ba'a; amma wadansu kuma sun ce, “Za mu saurare ka kuma, a kan wannan maganar.”

Read Ayyukan Manzanni 17Ayyukan Manzanni 17
Compare Ayyukan Manzanni 17:19-32Ayyukan Manzanni 17:19-32