Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 17

Ayyukan Manzanni 17:18-21

Help us?
Click on verse(s) to share them!
18Amma wadan su Abikuriyawa da masana sun yi karo da shi. Wadansun su na cewa, “Menene wannan sakaren ke cewa?” Wadansu kuma sun ce, “Da alama mai wa'azi ne na wasu alloli dabam,” domin yana wa'azin Yesu da tashin sa daga matattu.
19Suka dauki Bulus zuwa Tudun Arasa, suna cewa, “Ko za ka sanar mana da wannan sabuwar koyaswar taka?
20Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma'anar su.”
21(Atiniyawa da bakin da ke cikinsu, suna ba da lokacin su ga fadin sabobbin abubuwa da sauraron su).

Read Ayyukan Manzanni 17Ayyukan Manzanni 17
Compare Ayyukan Manzanni 17:18-21Ayyukan Manzanni 17:18-21