Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 17

Ayyukan Manzanni 17:1-15

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Bayan sun wuce biranen Amfibolis da Aboloniya, sun iso birnin Tasalunika, in da akwai wata majami'ar Yahudawa a wurin.
2Bulus, kamar yadda ya saba, ya nufi wurinsu, yana tattaunawa da su har Asabaci uku, daga cikin littattafai.
3Bulus ya bude littattafai yana bayyana masu cewa, dole ne Almasihu ya sha wahala, ya kuma tashi daga matattu. Ya ce, “Wannan Yesu kuwa da nake sanar maku, shine Almasihu”.
4Wasu Yahudawa sun yarda, sun bi Bulus da Sila, da wadansu Helenawa, da Shugabannin Mata da jama'a da yawa.
5Yahudawan da basu ba da gaskiya ba suka cika da kishi, suka dauki wadansu 'yan ta'adda daga cikin kasuwa, suka tada tarzoma cikin birnin, mutane da yawa na bin su. Sun kai hari a gidan Yason, da niyyar fitar da Bulus da Sila a gaban jama'a.
6Amma da ba su ga Bulus da Sila ba, suka ja Yason da wasu 'yan'uwa masu bi zuwa gaban mahukuntar birnin, suna cewa, “Wadannan ne fa masu ta da zaune tsaye, gashi sun zo mana.
7Wadannan mutane da Yason ya marabta, sun saba wa dokokin Kaisar; Suna cewa akwai wani sarki mai suna - Yesu.”
8Da taron jama'a, da mahukuntan birnin suka ji haka, sun damu.
9Bayan da sun amshi kudi daga wurin Yason da sauran 'yan'uwan, sai suka sake su.
10A wannan daren, 'yan'uwa masu bi suka fitar da Bulus da Sila, suka aike su garin Biriya. Da isar su can, su ka nufa majami'ar Yahudawa.
11Mutanen Biriya daban suke da na Tasalunika, sun yarda da sakon Bulus da zuciya daya, suna kuma binciken littattafai kowace rana domin su tabbatar da sakon Bulus, ko gaskiya ne.
12Saboda haka mutane da yawa cikin su sun ba da gaskiya, tare da wadansu sannanun mata Helenawa da maza da yawa.
13Amma da Yahudawan Tasalunika suka ji cewa Bulus yana wa'azin kalmar Allah a Biriya, sun haura can, sun tada hankulan jama'a.
14Nan da nan, masu bi na Biriya sun dauki Bulus sun aika shi zuwa teku, an bar Sila da Timoti a Biriya tukuna.
15Wadanda sun fitar da Bulus, sun kai shi har zuwa birnin Atina. Bulus ya ba su sako, su fada wa Sila da Timoti suyi hanzari su same shi.

Read Ayyukan Manzanni 17Ayyukan Manzanni 17
Compare Ayyukan Manzanni 17:1-15Ayyukan Manzanni 17:1-15