Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 16

Ayyukan Manzanni 16:19-35

Help us?
Click on verse(s) to share them!
19Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar shigar kudinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su cikin kasuwa suka kai su gaban mahunkunta.
20Da suka kai su Kotu, suka ce, “Wadannan mutane Yahudawa ne, suna kawo tashin hankali a birninmu.
21Suna koyar da abubuwa da ba su karbuwa a gare mu, balle mu aikata, a matsayinmu na Romawa.”
22Sai jama'a gaba daya sun tayar wa Bulus da Sila; alkalan kuma sun yage rigunansu, sun ba da umarni a duki Bulus da Sila da bulala.
23Bayan dukan, an jefa su Bulus a kurkuku, an ba mai tsaron kurkukun umurni ya kulle su da kyau, kada su gudu.
24Shi kuma ya yi hakanan, ya sa masu sarkoki a kafafun su, kamar yadda aka umurce shi.
25Da tsakar dare, Bulus da Sila suna yin adu'a, su na raira wakoki ga Allah, sauran 'yan sarkar su na jin su.
26Nan da nan sai ga wata girgizar kasa, wadda ta sa ginshikan kurkukun sun kadu, nan da nan kofofin kurkukun sun bude, 'yan sarka kuma, sarkokin su sun karkatse.
27Mai tsaron kurkukun ya tashi daga barci ya ga kofofin kurkukun a bude, ya zaro takobi, zai kashe kan sa, a tunanin sa, 'yan sarkar sun gudu.
28Amma Bulus ya ta da murya da karfi, ya ce, “kada kayi wa kanka barna, domin dukan mu muna nan”.
29Mai tsaron kurkukun ya aika a kawo fitila, ya shiga ciki a gurguje da rawan jiki, ya fadi a gaban Bulus da Sila,
30ya fitar da su waje ya ce, “Shugabanni, me ya kamata in yi domin in tsira?”
31Sun ce masa, “ka ba da gaskiya ga Yesu Ubangiji, da kai da gidan ka, za ku sami tsira”.
32Bulus da Sila suka fada masa maganar Ubangiji, tare da iyalinsa.
33Shi mai tsaron kurkukun ya dauke su cikin daren, ya wanke raunukansu, an kuma yi masa Baftisma nan da nan tare da iyalinsa.
34Ya kai Bulus da Sila gidansa, ya ba su abinci. Murna ta cika gidan mai tsaron kurkukun, domin iyalin sa duka sun ba da gaskiya ga Allah.
35Da gari ya waye, alkalai sun ba da sako a saki Bulus da Sila.

Read Ayyukan Manzanni 16Ayyukan Manzanni 16
Compare Ayyukan Manzanni 16:19-35Ayyukan Manzanni 16:19-35