Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 16

Ayyukan Manzanni 16:10-39

Help us?
Click on verse(s) to share them!
10Bulus, da ganin haka, ya kama hanya zuwa Makidoniya, da tunanin Allah ne ya ke so su kai wa mutanen Makidoniya bishara.
11Da barin Taruwasa, Bulus da kungiyarsa sun shiga jirgin ruwa zuwa Samutaraki, da gari ya waye kuma sun tafi Niyafolis;
12Daga nan kuma suka tafi Filibi, birni na Makidoniya, mai muhimmanci ne a yankin Roma, in da mun yi zango kwanaki da dama.
13Ranar Asabaci mun je kofar gari, gefen rafi, da tunanin samun wurin addu'a. Mun zauna mun kuma yi magana da matan da sun taru a wurin.
14Wata mace mai suna Lidiya, 'yar kasuwa ce a birnin Tiyatira, mai bautar Allah ce, ta saurare mu. Ubangiji ya bude zuciyarta, ta mai da hankali ga maganar da Bulus ke fadi.
15Sa'anda da aka yi mata Baftisma tare da mutanen gidanta, ta ce da mu, “Idan kun dauke ni mai bautar Allah, ku zo gidana ku zauna.” Sai ta rinjaye mu.
16A daidai wannan lokaci, muna tafiya wurin addu'a, wata yarinya mai ruhun duba ta hadu da mu. Iyayen gijinta na arziki da ita sosai.
17Tana bin Bulus, tare da mu, tana fadi da murya mai karfi cewa, “Wadannan mutanen, bayin Allah mafi daukaka ne, suna sanar maku hanyar ceto ne”.
18Ta dauki kwanaki tana haka. Amma Bulus ya yi fushi da ita ainun, ya juya ya umarci ruhun, ya ce, “Na umarce ka, ka rabu da ita a cikin sunan Yesu Almasihu”. Ruhun ya yi biyayya ya rabu da ita nan take.
19Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar shigar kudinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su cikin kasuwa suka kai su gaban mahunkunta.
20Da suka kai su Kotu, suka ce, “Wadannan mutane Yahudawa ne, suna kawo tashin hankali a birninmu.
21Suna koyar da abubuwa da ba su karbuwa a gare mu, balle mu aikata, a matsayinmu na Romawa.”
22Sai jama'a gaba daya sun tayar wa Bulus da Sila; alkalan kuma sun yage rigunansu, sun ba da umarni a duki Bulus da Sila da bulala.
23Bayan dukan, an jefa su Bulus a kurkuku, an ba mai tsaron kurkukun umurni ya kulle su da kyau, kada su gudu.
24Shi kuma ya yi hakanan, ya sa masu sarkoki a kafafun su, kamar yadda aka umurce shi.
25Da tsakar dare, Bulus da Sila suna yin adu'a, su na raira wakoki ga Allah, sauran 'yan sarkar su na jin su.
26Nan da nan sai ga wata girgizar kasa, wadda ta sa ginshikan kurkukun sun kadu, nan da nan kofofin kurkukun sun bude, 'yan sarka kuma, sarkokin su sun karkatse.
27Mai tsaron kurkukun ya tashi daga barci ya ga kofofin kurkukun a bude, ya zaro takobi, zai kashe kan sa, a tunanin sa, 'yan sarkar sun gudu.
28Amma Bulus ya ta da murya da karfi, ya ce, “kada kayi wa kanka barna, domin dukan mu muna nan”.
29Mai tsaron kurkukun ya aika a kawo fitila, ya shiga ciki a gurguje da rawan jiki, ya fadi a gaban Bulus da Sila,
30ya fitar da su waje ya ce, “Shugabanni, me ya kamata in yi domin in tsira?”
31Sun ce masa, “ka ba da gaskiya ga Yesu Ubangiji, da kai da gidan ka, za ku sami tsira”.
32Bulus da Sila suka fada masa maganar Ubangiji, tare da iyalinsa.
33Shi mai tsaron kurkukun ya dauke su cikin daren, ya wanke raunukansu, an kuma yi masa Baftisma nan da nan tare da iyalinsa.
34Ya kai Bulus da Sila gidansa, ya ba su abinci. Murna ta cika gidan mai tsaron kurkukun, domin iyalin sa duka sun ba da gaskiya ga Allah.
35Da gari ya waye, alkalai sun ba da sako a saki Bulus da Sila.
36Mai tsaron kurkukun kuwa ya sanar wa Bulus wannan magana ta alkalan, saboda haka ya ce wa Bulus, “Ku tafi cikin salama”.
37Amma Bulus ya ce masu, “Sun yi mana duka a fili a gaban mutane mu da muke Romawa, ba a kashe mu ba, sun kuma sa mu a kurkuku; suna koran mu a asirce? Su zo da kansu su fitar da mu.
38Masu tsaron kurkuku sun mayar da maganar Bulus ga alkalan, wanda ya sa sun firgita, da jin cewa Bulus da Sila Romawa ne.
39Alkalai da kansu sun zo sun roki Bulus da Sila; da suka fitar da su daga kurkukun, sun ce wa Bulus da Sila su bar birnin.

Read Ayyukan Manzanni 16Ayyukan Manzanni 16
Compare Ayyukan Manzanni 16:10-39Ayyukan Manzanni 16:10-39