Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 16

Ayyukan Manzanni 16:1-9

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Bulus ya kuma isa Darbe da Listira, in da akwai wani almajiri mai suna Timoti a wurin, dan wata Bayahudiya wadda ta ba da gaskiya; ubansa kuwa Baheline ne.
2Ana maganar kirki a kansa ta bakin 'yan'uwa da ke Listira da Ikoniyan.
3Bulus ya yi wa Timoti kaciya, domin yana so su yi tafiya tare, domin kuma saboda Yahudawan da ke wurin, sun san cewa ubansa Baheline ne.
4Suna shiga cikin biranen, suna yi wa iklisiyoyi gargadi da su yi biyayya da umurnan da Manzanni da dattawa suka rubuta a Urushalima.
5Bangaskiyar iklisiyoyi kuwa ta karu, ana kuma samun karuwa na wadanda suke ba da gaskiya kowace rana.
6Bulus da abokan aikin sa sun shiga cikin lardin Firigiya da Galatiya, tun da Ruhu Mai Tsarki ya hana su wa'azin kalmar a cikin yankin Asiya.
7Sun zo kusa da Misiya, da nufin shiga cikin Bitiniya, Ruhun Yesu ya hana su.
8Da suka ratse ta cikin Misiya, sai suka shiga birnin Taruwasa.
9Bulus ya ga wahayi cikin dare, wani mutumin Makidoniya na kiransa, yana cewa. “Ka zo Makidoniya ka taimake mu”.

Read Ayyukan Manzanni 16Ayyukan Manzanni 16
Compare Ayyukan Manzanni 16:1-9Ayyukan Manzanni 16:1-9