Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 15

Ayyukan Manzanni 15:8-23

Help us?
Click on verse(s) to share them!
8Allah, wanda ya san zuciya, ya yi masu shaida, ya kuma basu Ruhu Mai Tsarki kamar yadda ya yi mana;
9kuma bai bambanta mu da su ba, ya tsabtace zuciyarsu ta wurin bangaskiya.
10To, saboda haka don me kuke gwada Allah, kuna sa wa almajirai nauyi a wuya wanda ubanninmu duk da mu ba mu iya dauka ba?
11Amma mun gaskanta za mu samu ceto ta wurin alherin Ubangiji Yesu, kamar yadda suke.”
12Dukan taron jama'ar suka yi shiru sa'adda suke sauraron sakon shaidar da mamakin abin da Allah ya yi ta wurin Bulus da Barnaba a cikin al'ummai.
13Bayan sun gama magana, Yakubu ya amsa, ya ce, “'Yan'uwa, ku ji ni.
14Saminu ya fada yadda Allah ya fara nuna jinkai ga al'ummai domin ya dauke jama'a daga cikinsu domin sunansa.
15Maganar annabawa ta yarda da wannan, kamar yadda yake a rubuce,
16'Bayan wadannan abubuwa zan dawo, zan gina gidan Dauda wanda ya fadi kasa; in sake gina bangonsa, in tsayar da shi,
17saboda sauran jama'a su nemi fuskar Ubangiji, har da al'ummai da ake kira da sunana.
18Wannan shine abin da Ubangiji ya fadi, shi wanda ya yi wadannan abubuwa da aka sani tun zamanin da.
19Saboda haka, a gani na kada mu matsa wa al'umman da suka juyo gun Allah;
20amma zamu rubuta masu da cewa, su guje wa gumaka da zina da faskanci da maye da cin mushe.
21Tun zamanin da akwai mutane a kowanne birni wadanda suke wa'azi da karatun Musa a majami'u kowanne Asabaci.”
22Sai ya yi wa manzanin kyau su da dattawa da dukan iklisiyar su zabi Yahuza da Barnaba da Sila da dattawan iklisiya a tura su Antakiya tare da Bulus da Barnaba.
23Sai suka rubuta wasika, “Manzani da dattawa da 'yan'uwa zuwa ga al'ummai 'yan'uwa a Antakiya da Suriya da Kilikiya, gaisuwa mai yawa.

Read Ayyukan Manzanni 15Ayyukan Manzanni 15
Compare Ayyukan Manzanni 15:8-23Ayyukan Manzanni 15:8-23