Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 14

Ayyukan Manzanni 14:3-12

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Suka zauna a wurin na tsawon lokaci, suna yni maganarsu gabagadi da ikon Ubangiji, yana kuma shaidar sakon alherinsa. Ya yi wannan ta wurin alamu da al'ajibai ta hannun Bulus da Barnaba.
4Saboda haka mutanen garin sun rabu: wadansun su suka bi ra'ayin Yahudawa, wasu kuwa sun bi manzannin.
5Al'umman garin da Yahudawa sun nemi jan hankali shugabanninsu, don su wulakanta Bulus da Barnaba, su jajjefe su,
6da suka gane haka suka gudu zuwa biranen Likoniya, Listira da Darbe, da garuruwa wadanda ke kewaye da su,
7a can suka yi wa'azin bishara.
8A Listira akwai wani wanda ke zaune bai taba tashi da kafafunsa ba, don shi gurgu ne tun daga haihuwa.
9Wannan mutumin ya ji Bulus yana magana. Bulus ya kafa masa ido, ya gane mutumin na da bangaskiya da za a warkar da shi. Sai ya ce masa da murya mai karfi, “Tashi ka tsaya akan kafafunka”
10Sai mutumin ya yi tsalle ya fara tafiya da kafafunsa, yana yawo.
11Da jama'an garin sun ga abin da Bulus ya yi, suka tada muryarsu suna cewa da Likoniyanci, “Ai alloli sun ziyarce mu daga sama, da kamanin mutane.”
12Suna kiran Barnaba da sunan “Zafsa,” Bulus kuwa suka kira shi da sunan “Hamisa” domin shine yafi yin magana.

Read Ayyukan Manzanni 14Ayyukan Manzanni 14
Compare Ayyukan Manzanni 14:3-12Ayyukan Manzanni 14:3-12