Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 14

Ayyukan Manzanni 14:12-18

Help us?
Click on verse(s) to share them!
12Suna kiran Barnaba da sunan “Zafsa,” Bulus kuwa suka kira shi da sunan “Hamisa” domin shine yafi yin magana.
13Sai firist din zafsa wanda dakin yin masa sujada na kofar birni; ya kawo bijimai biyu da furannin da aka saka su kamar gammo; shi da jama'arsa suna so su yi masa hadaya.
14Amma da manzannin, wato Barnaba da Bulus, su ka ji labarin, suka yage rigunansu, suka hanzarta zuwa gun taron mutanen.
15Suna ta cewa, “Kuji! Ku mutane don me kuke wannan abin? Mu fa mutane ne kamarku. Mun kawo maku labari mai dadi ne, da cewa, ku rabu da abubuwa marar amfani, ku koma ga Allah mai rai, wanda ya hallici sama da kasa da teku da dukan abubuwa da ke cikinsu.
16A da dai ya bar mutane su yi abinda suka ga dama.
17Duk da haka, bai bar kansa ba tare da shaida ba, don yana bada abubuwa masu kyau, yana ba ku ruwan sama, lokatai masu albarka, ya cika ranku da abinci da farin ciki.”
18Duk da wadannan kalmomin da kyar, Bulus da Barnaba suka iya tsayar da su daga yi masu hadaya.

Read Ayyukan Manzanni 14Ayyukan Manzanni 14
Compare Ayyukan Manzanni 14:12-18Ayyukan Manzanni 14:12-18