Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 13

Ayyukan Manzanni 13:45-50

Help us?
Click on verse(s) to share them!
45Sa'adda Yahudawa suka ga taron jama'a, sai suka cika da kishi suna karyata abubuwan da Bulus ya fada suka kuma aibata shi.
46Amma Bulus da Barnaba sun yi magana gabagadi suka ce, “Dole ne a fara fada maku maganar Allah. Amma da yake kun ture ta, kun nuna baku cancanci rai madawwami ba soboda haka zamu juya ga al'ummai.
47Don haka Ubangiji ya umarce mu, cewa, 'Na sa ku haske ga al'ummai, saboda ku kawo ceto ga iyakar duniya.'”
48Da al'ummai suka ji haka, sai suka yi murna suka kuma yabi kalmar Ubangiji. Dukan wadanda aka kaddarawa samin rai madawwami suka tuba.
49Kalmar Ubangiji kuwa ta bazu a kowanne bangaren yankin.
50Amma Yahudawan suka zuga wadansu mata masu sujada, masu daraja da kuma shugabannin mazan garin. Wannan ya tayar da tsanani ga Bulus da Barnaba har suka fitar da su daga iyakar garinsu.

Read Ayyukan Manzanni 13Ayyukan Manzanni 13
Compare Ayyukan Manzanni 13:45-50Ayyukan Manzanni 13:45-50