27Saboda wadanda ke zaune cikin Urushalima, da masu mulkinsu, ba su gane shi ba, kuma sun cika fadin annabawa da a ke karantawa kowace ranar Asabaci ta wurin kashe shi.
28Duk da cewa ba su sami dalilin mutuwa a kansa ba, suka roki Bilatus ya kashe shi.
29Bayan sun gama duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka sauke shi daga giciye suka sa shi a cikin kabari.
30Amma Allah ya tashe shi daga matattu.
31Mutanen da suka zo tare da shi daga Galili da Urushalima kuwa suka yi ta ganinsa har kwanaki da yawa. Wadanan mutane kuma sune shaidunsa ga jama'a a yanzu.
32Mun kawo maku labari mai dadi game da alkawaran da aka yi wa kakkaninmu.