Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 13

Ayyukan Manzanni 13:1-10

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1A cikin iklisiyar da take Antakiya, akwai annabawa da malamai. Sune su Barnabas, Saminu (wadda ake kira Baki) da Lukiya Bakurame da Manayin (wanda aka yi renon su tare da sarki Hiridus mai mulki) da Shawulu.
2Sa'adda suke bauta wa Allah tare da azumi, sai Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku kebe mani Barnaba da Shawulu domin aikin da na kiraye su”.
3Bayan taron sun yi addu'a da azumi, sai suka sa masu hannu, su suka sallame su.
4Sai Shawulu da Barnabas suka yi biyayya da Ruhu Mai Tsarki suka tafi Sulukiya; daga nan suka ketare zuwa tsibirin Kuburus.
5Sa'adda suke garin Salami, suka koyar da maganar Ubangiji a majami'un Yahudawa, suna kuma tare da Yahaya Markus mai taimakonsu.
6Bayan sun zaga tsibirin duka har Bafusa, nan suka iske wani Bayahude mai suna Bar-yeshua mai tsafi kuma annabin karya.
7Wannan mai tsafin wanda ke tare da Makaddas, shi Sarjus Bulus mutum mai basira ne. Wannan kuwa ya kira Shawulu da Barnaba domin yana so ya ji maganar Allah.
8Amma Elimas “mai tsafi” (fasarar sunansa kenan) ya yi adawa da su; yana so ya baudar da Makaddashin daga bangaskiya.
9Amma Shawulu wanda ake ce da shi Bulus yana cike da Ruhu Mai Tsarki ya kafa masa ido.
10Sai ya ce, “Kai dan iblis, kana cike da kowace irin yaudara da mugunta. Kai abokin gabar kowanne irin adalci ne. Ba za ka daina karkata mikakkakun hanyoyin Ubangiji ba?

Read Ayyukan Manzanni 13Ayyukan Manzanni 13
Compare Ayyukan Manzanni 13:1-10Ayyukan Manzanni 13:1-10