Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 11

Ayyukan Manzanni 11:7-15

Help us?
Click on verse(s) to share them!
7Sai na ji murya tana ce da ni, “Tashi, Bitrus, yanka ka ci.”
8Na ce, “Ba haka ba, Ubangiji: gama babu abu mara tsarki ko mai kazanta da ya taba shiga bakina.”
9Amma murya ta amsa kuma daga sama cewa, “Abin da Allah ya kira mai tsarki, kada ka kira shi mara tsarki.”
10Wannan ya faru sau uku, sai dukan komai ya koma sama.
11Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni.
12Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin.
13Ya fada mana yadda ya ga mala'ika tsaye a cikin gidansa yana cewa “Aiki mutane zuwa Yafa, su kirawo Saminu wanda ake kira Bitrus.
14Zai gaya maku sakon da za ku sami ceto kai da dukan gidanka.”
15Da na fara magana da su, Ruhu Mai Tsarki ya sauko akansu kamar yadda ya sauko mana tun da farko.

Read Ayyukan Manzanni 11Ayyukan Manzanni 11
Compare Ayyukan Manzanni 11:7-15Ayyukan Manzanni 11:7-15