Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 10

Ayyukan Manzanni 10:3-7

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Wajen sa'a ta tara ga yini, an bayyana masa cikin wahayi mala'kan Ubangiji na zuwa gare shi sai mala'ikan ya ce masa, “Karniliyas!”
4Karniliyas ya zuba wa mala'ikan ido a tsorace ya ce “Menene, mai gida?” mala'ikan ya ce masa, “Addu'ar ka da taimakon ka ga talakawa ya kai sama matsayin sadaka abin tunawa a gaban Allah,
5“Yanzu ka aika mutane zuwa birnin Yafa su kawo mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus.
6Yana zama tare da Saminu majemi, wanda gidansa ke bakin teku.
7Da mala'ikan da ya yi magana da shi ya tafi, Karniliyas ya kira biyu daga barorin gidansa, da kuma soja guda mai bautar Allah daga cikin sojojin da suke masa hidima.

Read Ayyukan Manzanni 10Ayyukan Manzanni 10
Compare Ayyukan Manzanni 10:3-7Ayyukan Manzanni 10:3-7