Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 10

Ayyukan Manzanni 10:25-42

Help us?
Click on verse(s) to share them!
25Ya kasance sa'adda Bitrus ya shiga, Karniliyas ya sadu da shi kuma ya durkusa ya yi masa sujada.
26Amma Bitrus ya tashe shi yana cewa, “Tashi tsaye! Ni ma mutum ne.”
27A lokacin da Bitrus yake magana da shi, ya shiga ciki sai ya tarar da mutane da yawa sun taru a wuri daya.
28Ya ce masu, “Ku da kanku kun sani bai dace Bayahuden mutum ya yi ma'amulla ko ya ziyarci wani ko wata kabila ba. Amma Allah ya ce da ni kada in ce da kowa mara tsarki ko kazantacce.
29Wannan shine yasa na zo ba tare da musu ba, a lokacin da kuka kira ni. Don haka na tambaye ku me ya sa kuka aika in zo.”
30Karniliyas ya ce “Kwanaki hudu da sun wuce a daidai wannan lokaci, ina addu'a da cikin sa'a na tara (karfe uku) a gidana, sai na ga mutum tsaye a gabana da tufafi mai haske.
31Ya ce, “Karniliyas, Allah ya ji addu'ar ka, kuma taimakon ka ga talakawa ya tuna ma Allah da kai.
32Saboda haka ka aika da wani Yafa, ya kira maka mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. Yana zama a gidan Saminu majemi, da ke bakin teku.
33Idan ya zo, zai yi magana da kai.
34Sai Bitrus ya bude bakinsa ya ce, “Gaskiya, na fahimci Allah baya nuna bambanci.
35Maimakon haka, cikin kowace al'umma duk mai ibada kuma mai aikata adalci karbabbe ne a gare shi.
36Ku kun san sakon da ya aika wa mutanen Isra'ila, a lokacin da ya sanar da labarin mai kyau na salama ta wurin Yesu Kristi, wanda shine Ubangiji na duka.
37Ku da kanku kun san al'amuran da suka kasance, wanda ya faru cikin Yahudiya, farawa daga Galili, bayan sanarwar baftismar da Yahaya ya yi.
38Al'amura game da Yesu Banazare, yadda Allah ya kebe shi da Ruhu Mai Tsarki da iko kuma. Ya kuma ci gaba da aikin alheri da warkarwa ga dukan wadanda shaidan ya daure, domin Allah yana tare da shi.
39Mu shaidu ne ga dukan abubuwan da ya yi a kasar Yahudawa da cikn Urushalima, wannan Yesu wanda suka kashe, ta wurin giciye shi a akan itace.
40Wannan mutumin, Allah ya ta da shi rana ta uku ya kuma maishe shi sananne,
41ba ga dukan mutane ba, amma ga shaidun da Allah ya zaba tun da farko - mu kanmu, wadanda muka ci muka sha tare da shi bayan tashin sa daga matattu,
42Ya umarce mu mu yi wa mutane wa'azi mu kuma tabbatar cewa shine wanda Allah ya zaba ya yi shariya bisa masu rai da matattu.

Read Ayyukan Manzanni 10Ayyukan Manzanni 10
Compare Ayyukan Manzanni 10:25-42Ayyukan Manzanni 10:25-42