Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 10

Ayyukan Manzanni 10:17-21

Help us?
Click on verse(s) to share them!
17A yayin da Bitrus na cikin rudani game da ma'anar wahayin da ya gani, sai ga mutanen da Karniliyas ya aika suna tsaye a bakin kofar gidan, bayan sun tambayi hanyar zuwa gidan,
18Kuma suka yi sallama suna tambaya ko Saminu wanda ake kira Bitrus ya sauka a nan.
19A yayin da Bitrus yana kan tunani akan wahayin, Ruhu ya ce masa, “Duba, mutane uku na neman ka.”
20Tashi ka sauka ka tafi tare da su. Kada ka yi jinkirin tafiya tare da su, domin Nine na aike su.”
21Bitrus kuwa ya sauko wurin mutanen ya ce, “Ni ne wanda kuke nema. Me ya sa kuka zo?”

Read Ayyukan Manzanni 10Ayyukan Manzanni 10
Compare Ayyukan Manzanni 10:17-21Ayyukan Manzanni 10:17-21