Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 10

Ayyukan Manzanni 10:10-19

Help us?
Click on verse(s) to share them!
10Sai ya ji yunwa kuma yana bukatar wani abinda da zai ci, amma a yayin da mutanen na dafa abinci, sai ya ga wahayi.
11Sai ya ga sararin sama ya bude kuma wani tasa na saukowa, wani abu kamar babban mayafi yana saukowa zuwa duniya, ana zuro shi ta kusuryoyinsa hudu.
12A cikinsu kuwa akwai dukan halitun dabbobi masu kafa hudu da kuma masu rarrafe a duniya da tsunstayen sama.
13Sai murya ta yi magana da shi; “Tashi, Bitrus, yanka ka ci”
14Amma Bitrus ya ce “Ba haka ba, Ubangiji, gama ban taba cin abu mara tsarki ko mai kazanta ba.”
15Amma muryar ta sake zuwa masa karo na biyu kuma; “Abinda Allah ya tsarkake, kada ka kira shi kazantacce.”
16Wannan ya faru sau uku; nan da nan sai aka dauki tasar zuwa sama.
17A yayin da Bitrus na cikin rudani game da ma'anar wahayin da ya gani, sai ga mutanen da Karniliyas ya aika suna tsaye a bakin kofar gidan, bayan sun tambayi hanyar zuwa gidan,
18Kuma suka yi sallama suna tambaya ko Saminu wanda ake kira Bitrus ya sauka a nan.
19A yayin da Bitrus yana kan tunani akan wahayin, Ruhu ya ce masa, “Duba, mutane uku na neman ka.”

Read Ayyukan Manzanni 10Ayyukan Manzanni 10
Compare Ayyukan Manzanni 10:10-19Ayyukan Manzanni 10:10-19